Wasanni

Barcelona da Madrid zasu kara a wasan El Classico

El-classico, Lagos
El-classico, Lagos RFI Hausa

Yau ake saran fara wasan El Classico na farko a kakar shekarar 2020 zuwa 2021 inda Barcelona zata karbi bakuncin Real Madrid.Wannan wasa na zuwa ne a mako na 7, sabanin yadda aka saba a gani a shekarun baya lokacin da ake yin sa lokacin da wasannin sun yi nisa.

Talla

Yanzu haka a tebur Real Madrid ke matsayi na 3 da maki 10 a bayan kungiyoyi irin su Real Sociedad da Villareal, yayin da Barcelona ke matsayi na 10 da maki 7, ko da yake tana da bashin wasanni 2, yayin da Real Madrid ke da guda.

Yaya kuke kallon wannan wasa zai kaya? Muna dakon ra’ayoyin ku a shafin mu na Facebook.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.