Amurka-Zabe

Donald Trump ya kada kuri’ar sa yau a Florida

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump AP Photo/Julio Cortez

Shugaban Amurka Donald Trump kuma dan takara ya kada kuri’ar sa yau a Florida na zaben shugaban kasar da za’ayi ranar 3 ga watan gobe, yayin da ya shirya halartar wasu tarurrukan yakin neman zabe.

Talla

Rahotanni sun ce Trump ya kada kuri’ar sa ce a wata tashar zabe dake wani dakin karatu a inda yake da gida, bayan sauya mazabar sa dake New York.

Bayan kada kuri’ar cikin murmushi ya shaidawa manema labarai cewar ya kada wa ‘gayen’ nan Trump. Mataimakin sa Mike Pence ya kada ta sa kuri’a jiya a Indianapolis. Masu Sanya ido kan zaben na Amurka sun bayyana cewar ya zuwa yanzu mutane sama da miliyan 50 sun riga sun kada kuri’ar su a zaben da ake fafatawa tsakanin shugaba Donald Trump da tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.