Wasanni-Kwallon kafa

PSG zata yi tattaki zuwa Istanbul

Gasar cin kofin Europa
Gasar cin kofin Europa REUTERS/Eddie Keogh

Yayinda ake ci gaba da zaman doya da man ja tsakanin Faransa da Turkiya, yan wasan PSG sun soma nuna fargaba a jajuburin wasar da za su yi da kulob na kasar Turkiya Basaksehir a birnin Istanbul na kasar ta Turkiya.

Talla

Shugaban kulob na kasar ta Turkiyya a yayin da yake ganawa da manema labarai ya bayyana cewa Shugaban kungiyar ta PSG ,Nasser El Khelafi abokin sa ne,sabili da haka babu matsalla.

Kungiyar ta Besaksehir ce zakarar kasar, kuma a gobe laraba ne za a fafatawa tsakanin PSG da kungiyar dangane da gasar Europa.

Shugaban kungiyar ta kasar Turkiyya Goksel Gumusdag cikin raha da farin cikin ya na mai cewa babu abinda zai faru, suna farin cikin tarbar yan Faransa a wannan fafatawa da za a yi a filin wasa na Fatih Terim dake Istanbul ba taerda an baiwa yan kalo damar shiga wannan wasa ba.

Wasu daga cikin wasanninn da za a yi a gobe Laraba:Krasnodar daga Rasha za ta fafata da Chelsea daga Ingila.

Sevilla daga Spain za ta ketse reni da Rennes da za ta bakuci Sevilla a Italiya.

Club Burges daga Belgium za ta fafata da Lazio Roma daga Italiya.

Sai Dortmund daga Jamus da za ta buga wasa Zenith St Petersbourg daga Rasha.

Kar da mu manta da karawar bata tsakanin Juventus da Barcalona a gobe laraba ,karawar da ake sa ran za ta hada yan wasa Lionnel Messi da ya lashe ballon d’or sau shida da Christiano Ronaldo da ya lashe kwallon zinari sau biyar,yan wasan da rabon su hadu tun bayan ficewar Ronaldo daga Real Madrid a shekara ta 2018.

Sai dai wani abin lura da shi dan wasan Juventus Christian Ronaldo da aka gano ya na dauke da kwayar Covid 19,za a sake gudanar da gwaji a kan sa sa’o’I shida kafi a soma wasar,wanda indan har aka tabbatar da ba shi dauke da cutar zai taka leda,aksin haka ba zai halarci wasar ba.

Kazalika akwai wasa tsakanin Manchester United daga Ingila da RB Leipzig daga Jamus a gobe kenan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.