Turai-Covid-19

Mazauna Landan sun kaurace titunan kasar

Mazauna London dake Ingila sun kaurace titunan kasar kamar yadda hukumomi suka sanar domin dakile yaduwar cutar korona wadda ta sake dawowa cikin kasar.

Yankin Oxford Street,a kasar Birtaniya
Yankin Oxford Street,a kasar Birtaniya REUTERS/John Sibley/File Photo
Talla

Fitattun wuraren shakatawar kasar da suka hada fadar Buckingham da Dandalin Trafalgar da kuma biranen Manchester da Liverpool da aka saba ganin dandazon jam’a duk sun zama babu mutane a tituna domin mutunta dokar da aka kafa.

Rahotanni sun ce a yammacin jiya an samu arangama tsakanin masu adawa da dokar da jami’an tsaro a kusa da wata mashaya da kuma wasu sassan biranen London da Leeds.

A watan da ya gabata dai ne Fitaccen masanin kimiya a Birtaniya Farfesa Peter Horby, ya bayyana cewa, akwai yiwuwar sake kulle kasar baki daya saboda annobar coronavirus, amma ya ce za su yi tsayin-daka don ganin hakan bai tabbata ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI