Duniya

Azerbaidjan ta yi shelar kama garin Armenia

Kasar Azerbaijan ta bayyana cewar dakarun ta sun yi nasarar kama birnin Shusha daga hannun Yan awaren Armenia a Yankin Nagorno Karabakh a cigaba da fafatawar da ake tsakanin kasashen biyu, sai dai Armenia tayi watsi da ikrarin.

Yankin Nagorno Karabakh
Yankin Nagorno Karabakh AP Photo
Talla

Shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev ya sanar da kama garin lokacin da ya bayyana ta kafar talabijin sanye da kayan soji.

Kama garin Shusha zai zama gagarumar nasara ga yakin makwanni 6 da Azerbaijan ke yi a yankin Nagorno Karabakh wanda yan kabilar Armenia suka mamaye.

Sai dai jami’an gwamnatin Armenia sun yi watsi da kama garin, inda suka ce har yanzu ana can ana fafatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI