Iran-Amurka

Iran ta tace sinadarin uranium fiya da kima- MDD

Majalisar Dinkin Duniya tace kasar Iran ta tace sinadarin uranium har kashi 12 sabanin yarjejeniyar nukiliyar da kasar ta kulla da kasashen duniya.

Wasu daga cikin cibiyoyin nukiliyar kasar Iran
Wasu daga cikin cibiyoyin nukiliyar kasar Iran ATTA KENARE / AFP/File
Talla

Wani rahotan Hukumar yaki da yaduwar makamin nukiliya ta IAEA da kamfanin dillancin labaran Faransa ta samu, yace ya zuwa ranar 2 ga wannan wata, Iran ta tace kilogram 2,442 adadin da ya ribanya yadda aka amince mata a cikin yarjejeniyar da ta kulla.

Yarjejeniyar ta shekarar 2015 wanda shugaba Donald Trump ya janye Amurka daga ciki, tace baiwa Iran damar tace kilogram 300 na sinadarin uranium, amma sai ta saba mata.

Hukumar ta kuma ki amincewa da matsayin Iran kan kin gabatar da wani wuri da ake aikin nukiliyar, inda take cewa amsoshin da kasar ta bayar basu da tasiri.

Hukumar ta bukaci iran da ta gabatar da bayanan gaggawa dangane da gano sinadarin uranium din kamar yadda aka bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI