Turai-EU

Tunawa da sojojin da suka mutu yayin yakin duniya na 1

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Christophe Petit Tesson, Pool via AP

Jagororin siyasa da rundunonin soji da tsaffin sojoji da ma’aikatan lafiya har ma da ‘yan wasannin motsa jiki sun dakatar da abubuwan da suke yi a jiya don tunawa da sadaukar da sojojin da suka mutu yayin yakin duniya na 1 suka yi.

Talla

A Biranen Landan da Paris, shugaba Emmanuel Macron da Fira Minista Boris Johnson sun halarci bikin tunawa da ranar da aka sanya hannu a yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin duniya na daya.

Shugaba Macron ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa milyoyin sojoji ne suka sadaukar da rayuwarsu don Faransa.

Shima Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson ya hau shafinsa na Twitter inda ya wallafa cewa ‘’muna tunawa da dakarun mu maza da mata da suka sadaukar da rayuwar su.

Wannan shekarar ce ta dari da 2 dai-dai da aka sanya hannu a wannan yarjejniyar tsagaita wuta ta kawo karshen yakin duniya na 2, kuma shekaru 100 cur da binne wasu sojoji biyu na Faransa da Birtaniya da aka taho da gawarwakinsu daga filin daga, aka binne daya a Arc de Triomphe na Faransa, daya kuma a Westminster Abbey a Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.