Gabas ta tsakiya

Falesdinawa na adawa da ziyarar Mike Pompeo a Isra'ila

Mike Pompeo da mai dakin sa Susan a filin tashi dama saukar jirage na  Tbilissi
Mike Pompeo da mai dakin sa Susan a filin tashi dama saukar jirage na Tbilissi AP Photo/Patrick Semansky

Falesdinawa sun fito fili jiya sun yi Allah wadai da rangadin da sakataren waje na Amurka Mike Pompeo ya kai matsugunin yahudawa dake yammacin Gaban tekun Jordan jiya Alhamis, da kuma ikirarin Amurka na bata sunan duk masu tsanan yahudawa.

Talla

Nabil Abu Rudeineh, kakkakin Shugaban Falesdinawa Mahmud Abbas yace abin takaici ne nuna sonkai da Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump ke nunawa.

An dai gudanar da zanga-zangan nuna kyamar wannan rangadi da Pompeo ya kai.

Ana kallon  ziyarar ta Pompeo a matsayin marar tasiri, la’akari da cewar dukkanin kasashen da ya ziyarta sun taya abokin hamayyarsu na jam’iyyar Democrats Joe Biden murnar lashe zaben Amurka, kayen da har aynzu shugaba mai ci Donald Trump ke cigaba da nanatawa cewa an tafka magudi, tare da shan alwashin kalubalantar sakamakon zaben a shari’ance.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.