Wasanni

Ramos zai kauracewa fagen wasa

Kafatain din kungiyar Real Madrid Sergio Ramos zai kauracewa fagen wasa na kusan kwanaki 10 bayan rauni da ya samu a gwuiwar sa a yayin fafatawa tsakanin kungiyar Spain da Jamus a gasar cin kofin Nahiyoyi ranar talata da ta gabata.

Sergio Ramos na Real Madrid
Sergio Ramos na Real Madrid REUTERS/Sergio Perez
Talla

Kauracewar dan wasan Ramos na tamkar babban rashi ga kungiyar Real Madrid da zata karawa da Villareal a gobe asabar a gasar la liga, bayan haka Real za ta kuma ketse reni da Inter Milan ranar 25 ga wannan watan da muke cikin sa a gasar cin kofin zakaru.

A wannan wasa ta ranar talata da ta gabata Spain ta lallasa Jamus da ci 6 da nema.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI