Iran

Iran ta zargi Isra’ila da kisan masanin kimiyar nukiliyar Iran

Kisan masanin nukiliyar Iran Mohsen Fakhrizadeh
Kisan masanin nukiliyar Iran Mohsen Fakhrizadeh AP Photo

Iran ta zargi Isra’ila da kisan masanin kimiyar hada nukiliya Mohsen Fakhrizadeh sakamakon wani kazamin harin da wasu yan ta’adda suka kai masa jiya juma’a.

Talla

Ma’aikatar tsaron kasar tace Fakhrizadeh ya mutu ne a asibiti sakamakon munanan raunin da ya samu lokacin da maharan suka kai hari motar sa da kuma musayar wutar da aka samu tsakanin su da masu tsaron lafiyar sa.

Sanarwar tace jami’in dake shugabancin sashen bincike da kirkira na ma’aikatar tsaron Iran ya rasu a asibiti bayan da jami’an kula da lafiya suka kasa ceto rayuwar sa. Ministan harkokin wajen kasar Javad Zarif yayi Allah wadai da kisan wanda ya bayyana shi a matsayin harin ta’addanci.

Kasashen yammacin duniya na zargin kasar Iran da yunkurin samar da makamin nukiliya duk da matsayin Amurka da Israila dake cewa ba zasu taba bari ta samu makamin ba.

A yayin da hukumomin Iran ke zargin Isra’ila da wannan aika aikar, babban hafsan sojin kasar Manjao janar Mohammad Bagheri ya yi kashedin cewa za fa su rama wannan danyen aiki da aka aikata musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.