Duniya

Yan Sanda sun tarwatsa masu zanga a Santiago Chili

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a kasar Chili
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a kasar Chili REUTERS/Rodrigo Garrido

Dubban mutane ne suka fito a jiya juma’a a wata gaggarumar zanga-zang da ta gudana a Santiago Chili na kasar ta Chili tareda neman Shugaban kasar Sebastien Pinera ya sauka daga mukamin Shugabancin kasar.

Talla

Kusan mutane dubu 10 ne suka banzama saman manyan tittunan birnin dauke da aluna,suka kuma yi tattaki zuwa fadar gwamnatin kasar.

Jami’an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa kwala da ruwan zafi wajen tarwatsa masu bore, da suka sha alwashi ci gaba da gwagwarmaya har sai Shugaban ya sauka daga madafan ikon kasar ta Chili.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.