An yiwa Firaministan Isra'ila Allurar Korona
Wallafawa ranar:
Likitoci a Isra’ila sun yiwa Firaminsta Benjamin Nethanyahu allurar rigakafin cutar Korona.hakan na dada bude kofar soma yiwa yan kasar allurar rigakafin cutar ga baki daya.
Yan lokuta da yiwa Firaministan kasar Allurar, Benjamin Nethanyahu ya sheidawa manema labarai matakin da hukumomin Isra’ila suka dau na karfafa matakan kulawa musaman bangaren kiwon lahiya a filin tashi dama saukar jiragen sama da kuma gudanar da gwaji ga duk wani matafi daga ciki dama wajen kasar ga baki daya.
Firaministan kasar mai shekaru 71 ya isa asibitin Sheba dake yankin Ramat Gan daf da birnin Tel Aviv inda likitoci suka yi masa allurar Bion/Tech Pfizer kamar dai yada wani jami’in kamfanin dillancin labaren Faransa na Afp ya tabbatar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu