Turai

Gwamnatin Italiya ta kama hanyar rushewa

Giuseppe Conte,Firaministan Italiya
Giuseppe Conte,Firaministan Italiya Yara Nardi/Reuters

Gwamantin kasar Italia ta kama hanyar rushewa bayan da wasu abokanin kawance suka sanar da yin murabus daga cikin gwamnatin kasar.

Talla

Murabus din wasu Ministocin gwamnatin Italiya biyu ranar laraba na dab da kawo rarrabuwar kawuna ta fuskar siyasa,da shaka babu kan iya kawo rushewar gwamnatin kasar ta Italiya.

Murabus din MInistocin gwamnatin Guiseppe Conte ta saka shaku a zukatan da dama daga cikin yan siyasar kasar Italiya, jagoran Italiia Viva tsohon Firaministan kasar ta Italiya Matteo Renzi a wani taron manema labarai a ranar laraba ya jaddada ficewar ministocin jam’iyyar sa daga cikin wannan gwamnatin,Ministocin da suka hada da Teresa Bellanova dake jagorantar sashen noma da Elena Bonetti mai kula da iyali.

Gwamnatin Guiseppe Conte na fuskantar korafi daga masu dafa ma sa a fagen siyasa da tafiyar da mulki ba tareda ya nemi shawarar su ba,tsokaci daga tsohon Firaminista Matteo Renzi.

Tsokaci ya shafi musaman hanyoyi da gwamnati mai ci za ta yi amfani da su wajen kashe bilyan 200 na euros ,kudadden da kungiyar Turai za ta tallafawa kasar da su biyo bayan bulluwar cutar Coronavirus a kasar ta Italiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.