Turai

Jam'iyya mai mulki a Jamus ta zabi magajin Angela Merkel

Waziriyar Jamus Angela Merkel
Waziriyar Jamus Angela Merkel Hayoung JEON / POOL / AFP

Ya’an jam’iyya CDU mai mulki a Jamus sun zabi Armin Laschet a matsayin wanda zai gaji waziyar Jamus Angela Merkel a yau asabar bayan taron jam’iyyar CDU da abokiyar tafiyar ta CSU.

Talla

Angela Merkel ta share shekaru 15 a mukamin waziriyar kasar Jamus, tareda taka muhimiyar rawa tsawon lokaci da ta jagoranci gwamnatin kasar.

Ta na daga cikin jerin mata da suka shiga tarihi da kaffar dama a siyasar yankin Turai da Duniya ga baki daya.

Sabon Shugaban jam’iyyar ta CDU a Jamus Armin Laschet mai shekaru 59 na samu goyan bayan Angela Merkel, kuma hakan ya baiwa dan siyasar damar samu goyan bayan wakilan jam’iyyar 521 daga cikin wakilai 1001 dake karkashin hadin gwuiwar jam’iyyu da suka hada da CDU da CSU.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.