Wasanni

Zidane na cigaba da mamakin kin gayyatar Benzema dan yiwa Faransa wasa

Karim Benzema dan wasan Real Madrid
Karim Benzema dan wasan Real Madrid ANDER GILLENEA AFP/File

Mai horar da kungiyar Real Madrid Zinedine Zidane ya bayyana mamakin sa kan yadda kasar Faransa take cigaba da kin gayyatar Karim Benzema domin buga mata wasa. 

Talla

Yayin da yake tsokaci bayan bajintar da Benzema yayi wajen jefa kwallaye guda 2 da kuma baiwa Asensio domin jefa ta 3 a karawar da suka yi da Celta Vigo yau, Zidane yace ya kasa gane dalilin kin gayyatar dan wasan gaban.

Zidane na yabawa Karim Benzema
Zidane na yabawa Karim Benzema OSCAR DEL POZO AFP/Archives

Zidane yace shi dai bai fahimci dalilin kin gayyatar ba, ya kuma san mutane da dama ma basu fahimci haka, ganin yadda dan wasan ke cigaba da nuna bajinta.

A karawar yau Benzema ya jefa kwallaye 2 da suka kai kwallaye 10 da ya jefa a wasanni 10, matakin dake sa shi cikin yan wasan da suka yi fice wajen zirara kwallaye.

Bayan wasan na yau kungiyar Real Madrid zata saki yan wasan ta domin zuwa su yiwa kasashen su wasanni amma banda Benzema wanda Faransa ta daina gayyatar sa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.