Amurka

Shugaba Biden ya bayyana takaicin sa biyo bayan kisan mutane 10 a Amurka

Yankin Colorado,inda wani dan bindiga ya kashe mutane 10 a Amurka
Yankin Colorado,inda wani dan bindiga ya kashe mutane 10 a Amurka via REUTERS - CECIL DISHAROON

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana takaicin sa da kisan da wani dan bindiga ya yiwa mutane 10 a Colorado, cikin su harda jami’an dan Sanda guda.

Talla

Yayin da yake tsokaci akai, Biden yace ya bukaci Majalisar dokokin kasar ta amince da dokar takaita mallakar bindiga domin kare rayukan jama’a.

US- BIDEN- 2021-03-24

A shekara da ta 2020 da ta gabata jagororin addini da ‘yan siyasa da shahararrun mawaka da kuma fitattun mutane a fannonin wasanni, sun bi sahun dubban mutanen da ke zanga-zanga a ciki da wajen Amurka wajen yin tur da kisan George Floyd a birnin Minneapolis. A nasu bangaren Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Turai sun yi tur da yadda matsalar wariyar launi ke ci gaba a fannonin lafiya da Ilimi da kwadago a Amurka, tare da bayyana kaduwa kan yadda  aka halaka Floyd.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.