Chadi-Siyasa

‘Yan adawa sun bukaci a gudanar da zanga-zangar adawa da sojoji a Chadi

Janar Mahamat Idriss Déby Itno wurin jana'izar mahaifinsa, Idris Déby Itno. 23 afrilu 2021.
Janar Mahamat Idriss Déby Itno wurin jana'izar mahaifinsa, Idris Déby Itno. 23 afrilu 2021. REUTERS - STRINGER

Yau 28 ga watan Yuli kwanaki 100 kenan cur da Mahmat Idris Deby ya karbi ragamar mulkin kasar Chadi bayan mutuwar mahaifinsa Idris Debya a fagen daga.

Talla

To sai dai jam’iyyun adawa a kasar sun bayyana damuwa a game da yadda tsawon wadannan kwanaki har yanzu gwamnata ta gaza samar da yanayin da zai hada illahirin bangarorin al’umma don tattauna makomar kasar.

Roumadoumngar Felix Nialbé, wanda ya kasance jagoran ‘yan adawa a lokacin mulkin marigayi Idris Deby, ya ce akwai bukatar samar da yanayi don fara tattaunawa tsakanin gwamnatin mulkin soji da kuma saura rukuni na al’ummar kasar.

Yayin da wasu ke cewa akwai alamun samun mafita bayan da Kungiyar Tarayyar Afirka ta nada Basile Ikouebe matsayin manzon musamman da zai sa ido game da rikicin siyasar kasar ta Chadi, shi kuwa kawancen jam’iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula da ake kira Wakit Tama, kira ya yi ga ‘yan kasar da su gudanar da zanga-zanga a ranar alhamis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.