'Yan Malaysia sun bukaci gwamnatin kasar da ta sauka saboda gazawa

Shugaban gwamnati Malaisia
Shugaban gwamnati Malaisia REUTERS/Olivia Harris

A Malaysia duban dubatar mutane  ne suka yi na’am tareda kasancewa a zanga-zangar kyamar gwamnatin kasar tareda neman  ganin an rusa gwamnatin duk da cewa dokar hana tarruruka na aiki a kai sabilin da cutar covid 19.

Talla

Masu zanga-zangar sanye da bakakken tufaffi suna dauke da alluna dauke da sakonni dake nuna gazawar  gwamnatin kasar wajen magance tarin matsalloli da suka kuno kai tun bayan bulluwar cutar Covid 19 a Malaysia.

Taswirar kasar Malaysia
Taswirar kasar Malaysia DR 中文网络照片

Firaministan kasar  Muhyddin Yassin  duk da kokarin sa na ceto gwamnatin da yake jagoranta,dubban yan kasar na kalon sa a matsayin wanda ya rusa tattalin arzikin kasar ga baki daya ba tareda ya cinana wani abin azo a gani ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI