Human Right Watch ta zargi Facebook da sakonnin cin zarafin jama'a

dandalin sadarwa na Facebook,Instagram da WatsApp
dandalin sadarwa na Facebook,Instagram da WatsApp AP - Richard Drew

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Right Watch ta zargi Facebook da dandalinsa na Instagram da cire sakonnin cin zarafin Falasdinawa yayin tashin hankali tsakaninsu da Isra'ila a wannan shekara.

Talla

Zargin ya kara matsin lamba ga katafaren kamfanin  sadarwar ta duniya bayan da wani mai fallasa bayanan sirri ya bayyanawa 'yan majalisar dokokin Amurka a ranar Talata cewa akwai bukatar a daidaita tsarin kamfanin.

Dandalin Facebook
Dandalin Facebook Chris Delmas AFP/Archivos

Falasdinawa sun koka a bainar jama'a game da zargin yin kutse a shafukan sada zumunta a watan Mayu, yayin tashin hankali a birnin Kudus wanda ya rikide zuwa mummunan artabu na soji tsakanin kungiyoyin masu kishin Islama dake harba rokoki daga yankunan Falasdinawa, da Isra'ila wacce ta kaddamar da hare -hare ta sama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI