An soma zaben 'yan majalisun kasar Iraqi

Zaben 'yan Majalisun kasar Iraqi
Zaben 'yan Majalisun kasar Iraqi Ali NAJAFI AFP

Akalla mutane milyan 25 ne aka tanttance  za su kada kuri a zaben  yan majalisun dokkokin kasar Iraqi a yau Lahadi. Iraqi,kasar da  tattalin arzikinta ya durkushe da kashi 11, yayin da a gefe guda Asusun bada Lamuni na duniya IMF ya ce akalla kashi 40 na yawan al’ummar kasar da ya kai miliyan 40 na cikin kangin talauci.

Talla

Zaben dake a matsayin zakaran gwajin dafi ga gwamanatin Firaminista Moustafa al Kazimi wanda ya bayyana cewa ba shi da niyar sake tsayawa takara a wannan kasa da cin hantsi,rashawa da matsallar tsaro  suka kasance barazzana ga jama’a.

Daya daga cikin yan takara a zaben kasar Iraqi
Daya daga cikin yan takara a zaben kasar Iraqi Zaid AL-OBEIDI AFP/Archivos

A hukumance  a shekara ta 2022 ne ya dace a gudanar da wannan zabe,don kawo karshen   boren  jama’a dake zargin gwamnati da gazawa, a shekara ta 2019,yayi zanga-zangar  da ta gudana akalla mutane 600 ne suka bakuci lahira,wasu dubu 30 suka samu rauni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI